Connect with us

Labarai

Shugaba Bola Tinubu ya isa ƙasar Brazil

Published

on

Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Brasilia da ke ƙasar Brazil a yau Litinin domin ziyarar aiki ta kwana biyu a ƙasar daga birnin Los Angeles na Amurka, inda ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin kasar nan da takwarorin su na Brazil a filin jirgin Brasilia.

Ana dai sa ran Tinubu da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Sailva za su tatttauna su biyu ƙadai, sannan daga baya su fito su gudanar da taron manema labarai daga baya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakanin Najeriya da Brazil, inda ya ce a watan Maris na 2025, ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeninyar inganta noma da kasuwanci da tsaro da makamashi da ilimi da ma’adinai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!