Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ba zai taba sisin kwabo ba, daga daka biliyan daya na kudaden man wajen yaki da boko haram

Published

on

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan majalisar Dattawa Sanata Ita Enang, ya ce; shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba ko da sisin kwabo daga cikin dala biliyan daya na kudaden rarar man fetur wanda gwamnonin kasar nan su ka amincewa gwamnatin tarayya ta kashe domin yaki da Boko-Haram.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawar ya bayyana hakan ne a birnin Uyo babban birnin jihar Akwa-Ibom.

Ya ce, shugaban kasa ba zai baiwa sojoji ko da sisin kwabo daga cikin kudin ba har sai majalisun dokokin tarayya sun amince da hakan.

A watan Disamba da ta wuce ne kuma majalisar Dattawa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa ka da ya kashe kudaden batare da sahalewar majalisun dokokin tarayya ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!