Connect with us

Manyan Labarai

Shugaba Buhari ya bar gida Najeriya zuwa Afrika ta kudu

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar birnin tarayya Abuja zuwa kasar Afrika ta Kudu domin gudanar da wata ziyarar aiki.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Shugaba Buhari ya ya bar filin jirgi na Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 1:30 na rana a jirgin rundunar sojin saman kasar nan inda zai sauke shi a filin jirgin saman babban birnin kasar Pretoria.

Kafin dai tafiyar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari sai da ya jagoranci zaman majalisar na yau Laraba.

Ziyarar ta shugaba Buhari na zuwa ne kwanaki kadan  bayan da aka tattauna tsakanin shugaba Buhari da shugaban kasar ta Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa kan dawo da ‘yan Najeriya mazauna kasar sakamakon rikicin kin jinin baki da ‘yan kasar ke yi.

Yayin ziyarar, shugaba Buhari zai tattauna da shugaban kasar Cyril Ramaphosa kan batun walwalar ‘yan Najeriya mazauna can kasar Afrika ta kudu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,282 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!