Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai tsaye: Jam’iyyar PDP a Kano zata daukaka kara

Published

on

2:58pm

Kotun karbar kararrakin zabe anan Kano karkashin mai sharia Halima Shamaki ta kori karar da jam iyyar PDP da dan takarar gwamnan Kano a jam iyyar Abba kabir Yusuf suka shigar suna kalubalantar saamakon zaben gwamna daya gabata.

Mai sharia Halima Shamaki ta ayyana cewar shaidun da PDP ta gabatar sun yi rauni dan haka ta kori karar.

Hukuncin da lauyan APC Musa Abdullahi Lawan ya bayyana da cewa akwai gamsuwa matuka, koda yake lauyan PDP Bashir Yusuf Tudun Wuzurci yace ya zame musu dole daukaka kara.

2:30pm

Mai shari’a Halima Shamaki ta nemi alummar jihar Kano da su kwantar da hankalinsu, yayin da kuma  ta bukaci wadanda hukunci bai musu dadi ba da su garzaya zuwa kotun daukaka kara.

Haka zalika Mai shari’ar Shamaki ta ce masu shigar da kara suna hada tsaba da tsakuwa wajen gabatar da shedun su a don haka ya zama tilas ta kori karar.

A cewar Halima Shamaki  duk wanda hukuncin bai yi masa dadi ba to zai iya daukaka kara.

Kotun saurarran kararrakin zaben ta jadada nasarar da gwamnan jihar Kano ya samu a zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

Bayan da dan takarar jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf yake kalubalantar nasarar da Ganduje ya samu.

1:05 pm

Wasu mutane da basu sami damar shiga kotun ba a yayin da mai shari’a Halima Shamaki ke cigaba da karantowa

halima Shamaki dai na karanto hukunce-hukunce kan karar masu shigar da kara ke bukata wanda da dan takarar gwamnan a jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ke kalubanta na nasarar da Abdullahi Umar Ganduje yayi a zaben gwamnan wanda aka yi a ranar 9 ga watan Maris da ya gabata.

wasu ‘yan jaridu ke nan dake dakwan yadda za’a yanke shari’ar

12: 06am

Tun karfe 9 da rabi ne mai shari’a Halima Shamaki ta fara karantu hukuncin bukatun masu kara.

Ana hasashen cewar za’a kwashe Awanni 6 mai shari’a Halima Shamaki na karanto hukuncin shari’ar

11: 20am

Zaben Gwamnan Kano

Mai  jagoran tar Alkalan kotun saurarran kararrakin zaben gwamnan jihar Kano na cigaba da karantu bukatun masu kara yayin da ta fara mazabar Gama wacce ba’a kammala ba.

Halima Shamakin ta Ambato Alhaji Yunusa Dan gwani da sauran mutum 7 a matsayin shedun jam’iyyar PDP a zargin da suke na an tafka magudi a mazabar

Kai tsaye: Yadda shari’ar zaben Gwamnan Kano

Ganduje da Abba gida-gida

A halin yanzu mai shari’a Halima Shamaki ta fara karantu hukucin ta kan bukatun da masu kara da suka gabatar mata.

Haka zalika ma shari’a Halima Shamaki na cigaba da karanto bukatun masu kara tare da bada misalai.

Kai tsaye: Shari’ar Ganduje da Abba -Kotu ta shirya tsaf don yanke hukunci

An tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen harabar kotun saurarran karrakin zaben gwamnan jihar Kano yayin da jami’an tsaro suka hana amfani da duk ababan hawa da zai ratsa ta hanyar.

Freedom Radiyo ta kula cewa an sanya motocin jami’an tsaro a shataletalen fadar gwamnati da ya dagana zuwa titin Miller da kuma shalkwatar mabiya darikar Kwankwasiyya.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta hana duk wani gangamin magoya bayan ‘yan siyasa, don tabbatar da zaman lafiya.

Mai shari’a Halima Shamaki ta isa ofishin alkalai mintina da suka wuce, yayin da kuma nan da minti 25 ake sa ran cewar zata zauna don fara yanke shari’ar.

Ana kuma kyauta ta zaton cewar za’a kwashe  sa’o’I 6  ana yanke shari’ar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!