Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya bukaci yan Najeriya da su hanzarta don karbar katin zabensu

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan-Najeriya su hanzarta karbar katin zabensu na dindindin ka na kuma su zabi duk wanda su ke so yayin babban zaben kasa mai zuwa a badi.

Shugaba Buharin na wannan kira ne a daren jiya a fadarsa da ke Villa a Abuja, lokacin buda-baki tare da ma’aikatan bangaren Shari’a karkashin jagorancin Alkalin Kotun Koli mai Shari’a Olukayode Ariwoola.

Yayin mayar da martani kan jawabin da tsohon babban Jojin kasar nan Alfa Belgore ya yi na cewa Buhari ya na kaunar kasar nan kuma akwai bukatar samun mutanen kirki a tare da shi, shugaban kasa ya danganta nasarar zaben da ya yi a shekarar 2015 da fasahar zamani da aka yi amfani da ita.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaida cewa tuntuni ya shawarci gwamnoni su wayar da kan al’ummar Jihohinsu kan muhimmancin samun katin zabe na dindindin, tamkar katin shaidar ‘dan-kasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!