Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari ya isa jihar Kaduna don ganawa da jagororin addinai

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Jihar Kaduna don ganawa jagororin addinai da na Sarakunan gargajiya a Jihar biyo-bayan tashe-tashen hankula da aka fuskanta a kwanan nan.

Rikece-rikice sun sake barkewa ne a Jihar da suka yi sanadiyyar mutane ciki har da mai rike da Sarautar gargajiya Maiwada Galadima na masarautar Adara, da ake zargin masu satar mutane ne suka sace shi tare da hallaka shi.

Yamutsin ya fara a kauyen Kasuwar Magani da akalla mutane 55 suka mutu, sannan ya watsu zuwa cikin garin Kaduna har mutane 22 suka rasa rayukansu.

Daga bisani ne gwamnatin Jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga ta tsawon Sa’o’i 24, kafin sassauta ta a shekranjiya Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni jagororin addinan da Sarakuna gargajiyar Jihar suka halarci wurin da za a gudanar da ganawar wato Murtala Square, da aka baza jami’an tsaro da dama.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!