Connect with us

Labarai

Majalisar dokokin jihar Kano ta aika wasikar gayyata ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da aikawa da wasikar gayyata ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya gurfana gaban kwamitin binciken wasu faifan video da ake zargin gwamnan ya karbi na goro a gobe juma’a.

Wasikar mai dauke da kwanan wata talatin da daya ga watan jiya na Oktoba, jaridar solacebase ta ruwaito cewa an karbi sakon a gidan gwamnatin Kano a jiya Laraba.

Idan za a iya tunawa a rana ita yau alhamis 25 ga watan jiya na Oktoba ne, mawallafin jaridar Daily Nigeria da ta yada faifan video wanda a cikin sa a aka yi zargin cewa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na karbar na goro wato Jaafar-Jaafar, ya gurfana gaban majalisar, ya kuma ba da bahasi.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!