Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya jadadda tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da aiki ba dare ba rana har sai ya tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaba da kasancewar kasar nan dunkulalliya.

 

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ta cikin jawabi da ya gudanar da safiyar nan don bikin cikar kasar nan shekaru 58 da samun ‘yancin kai.

 

Ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa da kuma tabbatar da tsaro don kasancewar Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayi kasa daya dunkulalliya.

 

Muhammadu Buhari ya kuma jinjinawa jami’an tsaron kasar nan musamman sojoji da ‘yan sanda, sakamakon irin kokarin da suke wajen tsaron lafiya da dukiyar al’ummar kasa.

 

Shugaban kasar ya kara da cewa, dole ne ya yabawa dattijan da su ka yi ta fafutukan ganin kasar nan ta samu ‘yancin kai daga wajen turawar mulkin mallaka. Yana mai cewa har abada ba za a taba mantawa da gudumawar da suka bayar ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,603 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!