Connect with us

Kiwon Lafiya

An yi jana’izar matukin jirgin yakin sojin sama da yi yi hatsri

Published

on

An yi jana’izar matukin jirgin yakin rundunar sojojin sama na kasar nan Bello Muhammed Baba-Ari wanda ya rasa ransa sakamakon taho mu gama da wasu jirage da ke atisaye suka yi a jiya Juma’a.

Squadron leader Bello Muhammed Baba-Ari yana daya daga cikin matuka jirage uku da hatsarin ya ritsa da su a tsaunin Katamkpe da ke birnin tarayya Abuja.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar sojojin sama na kasar nan Air Commodore Ibikunle Daramola.

Sanarwar ta kuma ruwaito babban hafsan sojojin sama na kasar nan Air Marshall Sadique Abubakar na bayyana marigayin a matsayin jarumin soja da ya taka a bakin daga.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafar ta masa ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!