Kiwon Lafiya
Shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar nan da su karbe ikon makarantar sakandaren dapchi,a jihar Yobe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci rundunar sojin kasar nan da sauran jami’an tsaro da su karbe iko da harkokin tsaro a makarantar sakandaren koyar da sana’oi ta mata da ke Dapchi a jihar Yobe wanda kungiyar Boko-Haram ta kai hari a baya-bayan nan.
Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa a fadar Asorok a jiya Laraba.
A cewar sa shugaban kasar ya bada wannan umurnin ne bayan samun labarin batan wasu daga cikin daliban makarantar Sakandaren Dapchin casa’in da hudu sakamakon harin ‘yan boko-haram.
Ministan ya kara da cewa, shugaban kasar ya umurce shi da wasu takwarorinsa ministoci biyu da su kai ziyara makarantar a yau Alhamis domin nazari kan irin barnar da harin ‘yan boko haram ya haifar a makarantar da nufin daukar mataki na gaba.
Alhaji Lai Muhammed ya ce sauran ministoci biyu da za su rufa masa baya yayin ziyarar sun hada da: ministan tsaro Burgediya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya da kuma ministan kasashen waje Geoffrey Onyeama.