Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da shugaban majalisar Dattawa

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri  da shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da takwaransa na wakilai Yakubu Dogara a fadar Asorok da ke Abuja a daren jiya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka yada a shafin twitter na fadar shugaban kasa.

Ana dai tsammanin cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne a bangaren samar da mafita game da rahotannin kashe-kashe da ke faruwa a jihohin Benue da Taraba da Kaduna da kuma Rivers.

Rahotanni sun ce a na saran a yau Litinin shugaban kasar zai kuma gana da wata tawaga ta musamman daga jihar Benue wadanda suka hada da: shugabannin siyasa da kuma sarakunan gargajiya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!