Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce al’umma su zama cikin shirin cutar Sankarau

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bukaci al’ummar kasar nan su zama cikin shiri tare da sanar da hukumomi da zarar sun ji inda cutar Sankarau ta bulla, kasancewar karatowar lokacin barkewar cutar.

Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole ne ya yi wannan kira a garin Badin na Jihar Oyo a karshen makon da ya gabata, lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga manema labarai na fannin kiwon lafiya, dangane da shirye-shiryen da ma’aikatarsa ke yi wajen shawo kan wannan matsala da cutar Sankarau.

Ministen ya nanata bukatar ankarar da hukumomi cikin lokaci matukar aka samu barkewar cutar, kasancewar kasar nan ba ta da wadatattun kudin da za ta yi wa dukkannin al’ummar kasar Rigakafin cutar.

Farfesa Isacc Adewole ya buga misali da Jihar Kaduna sai dai da ya ke an dauki matakin gaggawa hakan ya sa aka shawo kan cutar cikin lokaci, amma ko da aka samu irin hakan a Jihar Zamfara mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon gaza sanar da hukumomi cikin lokaci, kuma aka gaza daukar matakan gaggawa a kai a shekarar da ta gabata.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,008 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!