Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari:ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Marigayi Chief Tony Anenih

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan tsohon shugaban kwamitin amintattu na Jam’iyyar PDP marigayi Chief Tony Anenih, wanda ya mutu jiya Lahadi a Abuja.

Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya shaida cewa shugaba Buharin ya aike da sakon ta’aziyyar ga al’ummar Jihar Edo da jam’iyyar PDP bisa mutuwar ta Tony Anenih.

Shugaban kasa ya bayyana Chief Tony Anenih a matsayin wanda ya bautawa kasa, kuma ya ba da gagarumar gudumnawa wajen ganin kasar nan ta tabbata kasa daya dunkulalliya.

Marigayi Tony Anenih ya shugabanci jam’iyyar NPN a mataki na Jiha sannan ya shugabanci SDP a mataki na kasa, sannan kuma tsohon Ministan ayyuka ne a kasar nan, ka na kuma kusa a ne a jam’iyyar PDP kafin mutuwarsa.

A jiya Lahadi ne di aka saka sanar da mutuwar Chief Tony Anenih a wani Asibiti mai zaman kansa da ke birnin tarayya Abuja, yana da shekaru 85 a Duniya.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!