Connect with us

Labarai

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa bisa kisan wadanda basu ji ba basu gani ba a Filato

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicin sa bisa kisan wadanda basu ji ba basu gani ba a jihar Filato, inda kuma ya ce gwamnatin sa ba zata sarara ba har sai ta tabbatar dukkanin masu hannu a cikin al’amarin sun fuskanci fushin kuliya.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi ta cikin shafin sa na twitter, inda ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici kuma mai sosa zuciya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma jajantawa al’ummar jihar da kuma iyalan wadanda aka rasa sakamakon wannan balahira.

Ta cikin shafin na sa na twitter shugaban kasar ya ce irin wannan kisa na ba gaira ba dalili da kuma asarar rayuka dake ci gaba da faruwa a jihar Filato abu ne mai matukar takaici da kuma ban tausayi.

A don haka Muhammadu Buhari ya ce ba zai samu sukunin ba har sai ya tabbatar wadanda suka aikata wannan al’amari an damke su an kuma hukunta su dai-dai da abin da suka aikata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!