Labarai
Shugaba Tinubu na hanyar dawowa Najeriya

Shugaban kasa Bola Tinubu zai dawo Najeriya yau Talata bayan kammala hutunsa a ƙasashen Birtaniya da Faransa.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga, ya fitar ya ce, Tinubu zai koma domin ci gaba da ayyukansa daga ranar 16 gwatan Satumba.
A makon da ya gabata ne Tinubu ya halarci liyafar cin abincin dare tare da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Élysée da ke birnin Paris.
Sanarwar ta ce shugabannin biyu sun tattauna batutuwan ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Faransa domin ci gaban ƙasashen biyu.
A ranar 4 ga watan Satumba ne Tinubu ya fara hutun na kwanakin aiki 10, a wani ɓangare na hutunsa na shekara da doka ta tanadar masa.
You must be logged in to post a comment Login