Labarai
Shugaba Tinubu na shirin saukaka kayan aikin Noma

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bai wa manoman Najeriya tabbacin samun sauƙin kayan aikin gona, musamman taki, kafin zuwan damina ta gaba damina.
Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da manema labarai, inda ya ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin tarayya na bunƙasa harkar noma da tabbatar da wadatar abinci a fadin ƙasar.
Sanata Yari, ya ce gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmad Tinubu za ta samar da taki mai yawa kuma a farashi mai rahusa domin bai wa manoma damar samun isasshen taki kafin zuwan damunar.
You must be logged in to post a comment Login