Labarai
Shugaba Tinubu na shirin yin ganawar gaggawa da manyan hafsoshin tsaro

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na shirin yin ganawar gaggawa da manyan hafsoshin tsaro dangane da halin da ake ciki na matsalar tsaro a wasu jihohin kasar nan.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa, sun tabbatar da cewa shugaba Tinubu zai gana da hafsoshin tsaro da kuma ministoci domin duba yadda za a magance matsalar tsaro, musamman a jihohin Filato, Benue da kuma Borno.
Ta cikin wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta, Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya zargi wasu gwamnoni da rashin yin amfani da kudaden harkar tsaro yadda ya kamata, duk da cewa suna karɓar makudan kudi a kowanne wata.
Haka kuma, Bwala ya bukaci gwamnonin da su kafa rundunonin tsaron yankuna a matakin kananan hukumomi da gundumomi domin tattara bayanan sirri da dakile hare-haren da suka zama ruwan dare.
You must be logged in to post a comment Login