Labarai
Shugaba Tinubu ya amince da kafa tawagar da za ta yi aikin haɗin gwiwa da Amurka

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da kafa tawagar Najeriya da za ta shiga wajen aikin haɗin gwiwa da Amurka, a karkashin kwamitin US Nigeria Joint Working Group, domin ƙarfafa dangantaka kan lamurran tsaro.
A cewar fadar shugaban kasa, wannan mataki na zuwa ne domin tabbatar da an samu tsari mai kyau na musayar bayanan sirri, horar da jami’an tsaro, da kuma ƙarfafa yaki da ayyukan ta’addanci a sassan ƙasar nan.
Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa, tawagar za ta haɗa manyan jami’an tsaro, masu ba da shawara kan harkokin diflomasiyya, da kwararru a bangaren leken asiri, domin tabbatar da an cika manufofin haɗin gwiwar yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login