Labarai
Shugaba Tinubu ya bayyana ƙudurin tantance shaidar ɗan ƙasa mai inganci

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa na gina tsarin tantance shaidar ɗan ƙasa mai inganci, da kuma tsaro, wanda zai bai wa kowane ɗan Najeriya damar shiga cikin tsarin ba tare da wariya ba.
Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a Alhamis ɗin makon na inda ya ce, tsarin tantance shaidar ta dan ƙasa watau National Identity Management System ta na da matuƙar muhimmanci wajen cimma burin ci gaban tattalin arziki da tsaro da kuma walwalar al’umma.
Tinubu ya ce, Gwamnatinsa da cikakken shiri na haɗa bayanan ‘yan ƙasa a wuri guda domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan gwamnati da samar da bayanai masu inganci don tsare-tsaren raya ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login