Labarai
Shugaba Tinubu ya gana da dangin waɗanda rikicin Jos ya shafa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da dangin waɗanda rikicin da ya afku a garin Jos ya shafa, yayin ziyarar jaje da ya kai jihar Plateau.
A yayin ziyarar, shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da ba su tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin.
Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan.
Rahotanni sun ce ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda hare-haren ke ƙaruwa a wasu sassan jihar.
You must be logged in to post a comment Login