Labarai
Shugaba Tinubu ya gana da Gwamna Fubara a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, a fadar mulki ta Aso Villa da ke Abuja.
Rahotonni sun bayyana cewa, Fubara ya isa Aso Villa da misalin ƙarfe 6:20 na yamma, inda kai tsaye ya shiga ofishin shugaban ƙasa domin yin ganawar sirri.
Wannan shi ne karo na farko da Fubara gana da shugaba Tinubu tun bayan dawo da shi ofis, bayan watanni shida na dakatarwa da gwamnatin tarayya ta yi masa tare da ayyana dokar ta baci a Jihar Rivers, wadda daga bisani aka soke ta a ranar 18 ga Satumba, 2025.
Sai dai bayan kammala ganawar tasu ba a bayyana batutuwan da suka tattauna ba.
You must be logged in to post a comment Login