Labarai
Shugaba Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a fadar mulki ta Villa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a Fadar Shugaban Ƙasar da ke babban bornin tarayya Abuja.
Ganawar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya gana da Archbishop Ignatius Kaigama na Katolikan Abuja, a wani yunƙuri na inganta dangantakar addinai da zaman lafiya a Najeriya.
Ko da yake ba a bayyana abin da suka tattauna ba, amma ganawar ba za ta rasa nasaba da ƙarfafa fahimtar juna tsakanin addinai da kuma bunƙasa haɗin kan ƙasa da ci gaba.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya bisa zargin cin zarafin Kiristoci.
You must be logged in to post a comment Login