Labarai
Shugaba Tinubu ya kira taron gaggawa na Majalisar ƙoli

Shugaban Bola Ahmad Tinubu ya kira taron gaggawa na Majalisar ƙoli ta ƙasa da hukumar ƴan sanda a yau Alhamis, domin tattauawa kan matsalar rashin tsaro.
Wannan mataki na zuwa ne sakamakon yadda matsalar tsaro ke kara kamari a sassan kasar, musamman hare-hare, satar mutane da kuma rikice-rikice da ke addabar al’umma.
A cewar majiyoyi daga fadar shugaban kasa, za a tattauna kan yadda gwamnati za ta kara karfafa jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru wajen yaki da ayyukan ta’addanci da rashin tsaro. Taron zai kuma duba batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar ‘yan kasa.
Majalisar ƙoli ta ƙasa na kunshe da tsoffin shugabannin ƙasa da gwamnonin jihohi da manyan jami’an gwamnati. Ana sa ran wannan taro zai samar da muhimman shawarwari da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login