Labarai
Shugaba Tinubu ya miƙa wa majalisa sunayen mutum 32 da yake son naɗa su jakadu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya miƙa wa majalisar dattawa sunayen mutum 32 da yake son turawa a matsayin jakadun ƙasar zuwa ƙasashen waje.
Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a yau Asabar ta ce shugaban ya nemi majalisar ta gagaggauta tantancewa da amincewa da mutanen.
Sunayen sun ƙunshi Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, da Reno Omokri, tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman.
A ranar Alhamis ne Tinubu ya nemi majalisar ta amince da tura jakadu zuwa Amurka da Ingila da Faransa.
Fiye da shekara biyu kenan da gwamnatin APC ƙarƙashin Tinubu ta yi wa jakadun ƙasar kusan 109 kiranye kuma tun daga lokacin wakilai ne ke tafiyar da ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashen waje.
You must be logged in to post a comment Login