Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya sauya tafiyarsa daga Ogun da zuwa birnin Jos domin yin jaje

Published

on

Shugaba Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jinkirta tafiyarsa da ya shirya yi zuwa  Jihar Ogun, domin kai ziyarar jaje zuwa birnin  Jos, sakamakon hare-haren da suka auku ranar Lahadi da ta gabata, waɗanda suka yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 27.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan.

Sanarwar ta ce,  daukan matakin ya biyo bayan ganawar da shugaban ya yi da gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, a Fadar Aso Rock da ke Abuja a yammacin Laraba nan, inda gwamnan ya yi masa bayani kan halin tsaron jihar.

Sanarwar ta ce shugaban ƙasar zai isa Jos yau domin jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Plateau kan hare-haren da suka faru a yankin Angwan Rukuba da ke Jos ta Arewa.

Daga nan, shugaban zai wuce Lagos domin gudanar da sallah Juma’ar na gobe sannan a Jibi Asabar 4 ga Afrilu zai wuce Jihar Ogun domin ƙaddamar da filin jirgin sama na Gateway International Cargo, tare da wasu jiragen kasuwanci guda biyu domin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da shigo da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!