Labarai
Shugaba Tinubu ya shirya don tarbar gawar tsohon shugaban kasa Buhari

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai tarbi gawar tsohon shugaban kasar nan a yau Talata a filin jirgin saman jihar Katsina, inda daga nan ne za a wuce da ita zuwa garin Daura dan yi masa sutura kamar yadda addinin muslinci ya tanada.
Gwamnatin tarayya ta sanar da gawar marigayin za ta iso kasar nan a yau da misalin karfe 12 na rana, inda ake saka ran za a gudanar da jana’izar sa milin karfe uku na yamma a gidan sa dake Daura.
Ministan sadarwa da wayar da kan jama’a, Muhammad Idris ya ce tuni aka kammala duk wasu tsare-tsare na binne gawar mamacin tare da kafa wani kwamiti na ma’aikatu hadin guiwa da gwamnatin jihar Katsina da zasu saka ido dan ganin komai ya tafi daidai.
Kwamitin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Sannata George Akume, da ya kunshi kususoshi daga ma’aikatar kudi da ta kasafi da tsare-tsaren tattalim arziki da tsaro da ma’aikatar ciki gida da shugaban ‘yan sanda da DSS fa sauran hukumomi.
You must be logged in to post a comment Login