Labarai
Shugaba Tinubu ya taya al’ummar musulmi murnar bikin Sallah

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar Idin karamar sallah, tare da rokon su ci gaba da amfani da darussan da suka koya a watan Ramadan wajen gina kasa.
Shugaban, ya kuma bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar da mai bashi shawara kan kafafen yada labarai Bayo Onanuga ya fitar.
Tinubu ya kuma bukaci musulmi su rika taimaka wa mabukata ba tare da la’akari da bambancin addini ba, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen karfafa zumunci da hadin kai tsakanin al’ummar kasa.
You must be logged in to post a comment Login