Labarai
Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaro su farauto wadanda suka kashe mutane a kasuwar Neja

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci ministan tsaro da babban hafsan tsaron ƙasar baya ga babban sifeton ƴansanda da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya su farauto tare da kama maharan Kasuwan Daji da ke jihar Neja, domin su fuskanci hukunci.
A ranar Asabar da maraice ne dai wasu mahara suka far wa ƙauyen Kasuwan Daji a jihar Neja inda suka kashe fiye da mutum 30 tare da sace wasu mata da ƙananan yara da ba a san adadinsu ba da kuma ƙona kasuwar da sace kayan abinci.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaron ƙasar su kuɓutar da mutanen da maharan suka sace.
Sanarwar ta ce ana zargin maharan sun taso ne daga jihohin Sokoto da Zamfara domin guje wa hare-haren da Amurka ta kai musu a jajiberin Kirsimeti.
You must be logged in to post a comment Login