Labarai
Shugaba Tinubu ya umarci Matawalle ya zauna a Kebbi har sai an kuɓutar da ɗaliban Maga

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi domin sanya ido tare da mayar da hankali kan aikin ceto dalibai mata 25 da ƴan bindiga suka sace a makarantar Sakandaren gwamnati da ke Maga, a Ƙaramar hukumar Danko Wasagu.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan kafafen yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar a Alhamis ɗin makon nan.
Haka kuma, sanarwar, ta ƙara da cewa, shugaba Tinubu, ya umarci Matawalle da ya zauna a jihar har sai an tabbatar da an kuɓutar da ɗaliban.
You must be logged in to post a comment Login