Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya yi wa ɗaurarru fiye da 80 afuwa

Published

on

Cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar ta ce, shugaba Tinubu ya yi amfani shawarwarin kwamitin da ya kafa kan yafe wa masu laifi, wanda ministan shari’a Lateef Fagbemi ya jagoranta.

 

Haka kuma shugaba Tinubu ya yafewa Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa, wanda aka yankewa hukuncin kisa bisa laifin cin amanar kasa a shekarar 1986, da Herbert Macaulay, da wasu ƙarin mutane 82 dake zaune a gidan gyaran hali.

 

Cikin waɗanda shugaban ya yafe wa har da Faruk Lawan Tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono na jihar Kano.

 

A ranar 23 ga watan Yunin 2021 ne wata babbar kotun tarayya ta zartar da hukuncin ɗaurin shekara bakwai kan Farouk Lawan , wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin tallafin mai a majalisar wakilai.

 

Daga baya wata kotu ta rage shekarun daga bakwai zuwa biyar bayan ya daukaka kara.

 

Hakan ya biyo bayan samunsa da laifin karbar cin hancin Dala 500,000 a wurin Femi Otedola, wani hamshakin dan kasuwa, domin wanke kamfaninsa daga badaƙalar tallafin mai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!