Labarai
Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya yau Litinin

Fadar shugaban kasa ta ce, shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya a yau Litinin bayan kwashe kusan mako uku da yin balagura.
Mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Idan za a iya tunawa tun a ranar 2 ga watan nan da muke ciki na Afurilu ne shugaba Tinubu ya fice daga Najeriya zuwa kasar Faransa, a wata ziyarar aiki, kamar yadda sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta bayyana.
You must be logged in to post a comment Login