Labarai
Shugaba Tinubu zai tafi Turkiyya ranar Litinin

Shugaban Kasa Bola Tinubu zai bar Abuja a yau Litinin don ziyarar aiki a turkiyya , a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce ziyarar zata mayar da hankali wajen hadin gwiwa a bangaren tsaro, ilimi, ci gaban zamantakewa, kirkire-kirkire, da kuma harkokin jiragen sama.
A ziyarar Shugaba Tinubu, ana sa ran ƙasashen biyu za su gudanar da shawarwari na siyasa da diflomasiyya, waɗanda suka mayar da hankali kan muradun da suka shafi kuɗi, sadarwa, ciniki, da saka hannun jari.
You must be logged in to post a comment Login