Labarai
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dawo Najeriya

A yau Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya sauka a Abuja, bayan wata huldar diflomasiyya a Japan da Brazil.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga, ya fitar jirgin shugaban kasa, wanda ya tashi daga sansanin sojojin sama na kasa da kasa na Brasília da karfe 12:57 na rana a agogon Najeriya ranar Laraba, ya iso da sanyin safiyar yau Alhamis.
Tinubu ya halarci bukin budewa da cikakken taron bunƙasa nahiyar Afirka mai karo na 9 mai taken Tokyo International Conference on African Development (TICAD9) a ranar 20 ga Agusta a Japan.
Ya gudanar da tarurrukan kasashen biyu kuma ya kammala taron tattaunawa da al’ummar Najeriya.
Bayan kammala TICAD 9, ya bar Yokohama Inda ya tsaya a birnin Los Angeles NA Amurka, daga bisani ya wuce birnin Brasília.
A Brazil, ya gana da shugaban kasar Luiz Inácio Lula da Silva da manyan jami’an Brazil.
Shugabannin biyu sun yi wata tattaunawa ta sirri tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda biyar.
Yarjejeniyar ta shafi harkokin sufurin jiragen sama da harkokin waje da kimiyya da fasaha da kuma noma da ma muhimman sassa a cikin tsarin ci gaban Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login