Labarai
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Saudiya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar gida Najeriya don halatar taron zuba jari na Future Investment Iniatiative a birnin Riyad na kasar Saudiya mai taken ‘’Menene mataki na gaba kan kasuwanci a duniya’’
A yayin ziyarar bayan da mai taimakawa shugaban kasa shawara kan kafafan yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar kwanaki biyu da dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kasar Russia, ana sa ran cewa za’a tattauna batutuwa masu muhimmanci don bunkasa kasuwancin kasar nan da ma tattalin arziki na Afrika ta yamma ciki har da kasar nan.
Daga cikin wadanda za su yi wa shugaban kasa rakiya akwai gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da Abubakar Bagudu na jihar Kebbi da Aminu Bello Masari na jihar Katsina.
Sauran su ne ministan al’amuran kula da kasashen waje Zubairu Dada da Ministan ciniki da zuba jari Niyi Adebayo da karamin Ministan man fetur Timipre Sylva da kuma Ministan sadarwa Ibrahim Pantami.