Connect with us

Labarai

Fadar shugaban kasa ta aike da ta’aziyar ta ga Iyalan Tafawa Balewa

Published

on

Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya aike da ta’aziyyar sa ga iyalan uwargidan marigayi Abubauakr Tafawa Balewa tsohon firaministan kasar nan Hajiya  Aisha Jummai Abubakar Balewa wace ta rasu a ranar Lahadin da ta gabata.

Sakon ta’aziyyar wacce ke dauke da sa hannun mai taimakawa shugaban kasa na mussaman kan yada labarai Malam Garba Shehu da ya fitar a Abuja.

Take cikin sanarwar wacce aka aikewa gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da kuma iyalan Abubakar Tafawa Balewa cewa shugaban kasa yayi addu’ar Allah ya jikan Marigayiya  Hajiya Jummai Tafawa Balewa, yayi mata rahama.

Haka zalika Malam Garba Shehu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha umarnin da a shirya jirgin da zai dauko gawar marigayiyar daga Lagos  zuwa jihar Bauchi, bayan da ta rasu a wani asibiti mai zaman kan sa a can.

Za’a dai  ayi jana’izzar  marigayiyar ne a yau Litinin ne a mahaifar ta dake jihar Bauchi.

Yayin da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad  ya bayyana rasuwar marigayiyar Hajya Aisha Jummai Tafawa Balewa a matsayin babban rashi ga jihar Bauchi ta kasa baki daya.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai taimakawa gwamnan kan kafafan yada labarai Muktari Gidado ya sanya wa hannu a jihar Bauchi.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!