Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaban kasa ya damka Amanar biliyan 183 a hannun Kanawa

Published

on

Bayan da ya gabatar da kasafin kudin badi a jiya Talata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kebe Naira Biliyan 100 ga ma’aikatar tsaro yayin da kasar nan ke fuskantar matsalolin tsaro da sace mutane da yin garkuwa da  mussaman ma a yankin Arewa maso yammacin kasar nan.

Mejo Janaral Bashir Salehi Magashi da ya fito daga nan jihar Kano ne ke jagorantar ma’aikatar a zango na biyu na wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yayin da kuma aka kebewa ma’aikatar gona Naira biliyan 83 bayan da gwamnatin tarayya ta rufe kan iyakokin ta a wani mataki na yin amfani da abubuwan da muke sarrafawa a cikin gida mussama kayayyakin abinci.

Alhaji Sabo Nanono  wanda yafito daga nan Kano shi ke kula da ma’aikatar gona a wa’adi na biyu na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yaya kuke kallon irin wadannan makudan kudaden da aka warewa ma’aikatun ganin an dora Amanar ne ga ‘yan asalin jihar Kano?

Majalisa:An samu hargitsi yayi gabatar da kunshen kasafin kudin badi

Gwamnatin Kano tayi watsi da zargin cewar gina gadar Dangi baya ckin kasafin kudin bana

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ministoci kan su je majalisun dokokin tarayya don kare kasafin kudi

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sami rakiyar wasu daga cikin ‘yan Majlisar zartarwa na kasa wajen gabatar da daftarin kudirin kasafin kudin badi, gahadakar  majalisar dokoki ta kasa.

Shugaba Buhari wanda ya fara jawabi ga hadakar majalisun da misalign karfe 2 da minti 3 na ranar yau Talata, ya gabatarwa majalisun daftarin kasafin kudin badi da yah aura Naira Tiriliyan goma 10.

Tun da fari majalisar zartarwa ta kasa ta mika daftarin kasafin kudin badi bayan da ta tsara akan Naira Tirilyan 10 da miliyan bakwai yayin da su kuma ‘yan Majalisar suka kara zuwa Tiriliyan 10 da miliyan talatin da uku.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce daftarin gwamnatinsa ta tsara kasafin ne a kan kudin harajin kayayyaki da na VAT, a don haka  ya zama tilas  a  kara yawan harajin daga kaso hudu zuwa 7.7

Hakan dai zai sanya gwamnati damar cike gibin fiye da naira tiriliyan biyu da ke kasafin kudin kasar da Muhammadu Buhari ya gabatatar a yau.

Muhammadu Buhari wanda ya gabatar da daftarin kasafin kudin a gaban zauren majalisar dokokin kasar, ya ce kasafin na 2020 ya haura na 2019 da kaso 9.7 cikin dari.

 

Yadda kowanne ma’aikatu Kasafin su zai kasance ga

  • Ma’aikatar Tsaro – naira biliyan 100
  • Ma’aikatar ayyukan gona – naira biliyan 83
  • Ma’aikatar Albarkatun ruwa – naira niliyan 82
  • Ma’aikatar kula da Ilimi – naira biliyan 48
  • Ma’aikatar Lafiya – naira biliyan 46
  • Hukumar Raya Arewa maso gabas – naira biliyan 38
  • Birnin tarayya – naira biliyan 28
  • Hukumar kula da yakin Neja Delta – naira biliyan 24
  • Sai kuma Majalisar dokoki – naira biliyan 125
  • Ma’aikatar Shari’a – naira biliyan 110
  • Ma’aikatar ayyuka da da gidaje – naira biliyan 262
  • Ma’aikatar Sufuri – naira biliyan 123
  • Hukumar ilmi a matakin farko UBEC – naira biliyan 112

 

Masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewar a bara dai a yayin gabatar da kasafin kudin bara an yi ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari Ihu kuma wannan shi ne  karon farko da zauren majalisa na yayi ta Sowa sai Baba sai Baba.

Wannan dai alama ce dake nuna dagantakar zaman lafiya tsakanin majalisar zartarwa da ta ‘yan majalisar.

Rahotanni sun bayana cewar  wannan ne karon farko da shugaban kasa Muhammadu ya  gabatar da daftarin kasafin kudi a kan akari saboda alakar da ke tsakanin majalisa da bangaren zartarwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!