Labarai
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Akpabio ya sake maka Natasha a gaban kotu

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya shigar da Sanata Natasha Akpoti ƙara a kotu kan zargin ɓata masa suna yana mai neman ta biya shi diyyar naira biliyan 200.
Sanata Natasha mai wakiltar jihar Kogi ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta samu damar bayyana hujjojinta kan zargin yunƙurin lalata da ta zarge shi da yi a baya.
A watan Fabrairun 2025 ne Natasha ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita bayan rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu, wanda ya kai ga dakatar da ita daga zaman majalisar na tsawon wata shida.
You must be logged in to post a comment Login