Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bukaci al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu

Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu, ya na mai cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da ingantuwar tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
Yayin isar da saƙon shugaban ƙasar, jim kaɗan bayan ganawa da shi, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris, ya ce shugaban ƙasar na cigaba da nazari, domin samar da mafita ga tsaro.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa, shugaban na ƙoƙarin fahimtar da ƙasashen duniya irin ƙoƙarin da Kasar ke yi wajen magance matsalar tsaron.
Ta cikin wani faifan bidiyon hirar da ministan ya yi da gidan talbijin na ƙasa, NTA ya wallafa, ministan ya ce, ko sauya shugabannin tsaron da Tinubu ya yi a makonni biyu da suka gabata na da nasaba da ingantuwar tsaron ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login