Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugabannin yan bindiga a Katsina sun yi saranda

Published

on

Wasu manyan shugabannin yan bindiga 26 da suka addabi jihar Katsina sun ajiye makaman yakin su tare da mika wuya a Alhamis din nan.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sanusi Buba ne ya bayyana hakan yayin da yake baja kolin shugabannin tare da mabiyansu wadanda suka ajiye makamai da alburusai.

Buba ya ce shugabannin ‘yan bindigar da kansu suka fito daga maboyarsu a cikin daji tare dayin tir da ayyukan da suke yi na fashi, kuma sun yi hakan ne ba tare da wani sharadi ba.

Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana sunayen shugabannin ‘yan bindigar da suka hadar da Sale Turwa, Mani Turwa, Ado Sarki da kuma Sani Mai-Daji.

Sanusi Buba ya gargadi sauran ‘yan bindiga masu tayar da kayar baya, wadanda suka ki mika wuya da su gaggauta sake tunani don samarwa kan su mafita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!