Connect with us

Labarai

Siyasar Kano: Shekarau ya yi tir da kalaman Kwankwaso da Abdullahi Abbas

Published

on

Tsohon gwamnan Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya yi martani ga tsohon gwamnan Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso da shugaban jam’iyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas.

A yayin ganawarsa da manema labarai a daren Lahadi Sanata Shekarau ya yi musu martani kan kalaman tunzura jama’a da aka same su da yi.

Game da Kwankwaso Shekarau ya ce, duk wanda ya nemi mata su ɗauko taɓarya a zaɓen gaba, to ya sanya matarsa riƙe da taɓarya a kan gaba ranar zaɓen.

Da ya juyo kan Abdullahi Abbas kuwa ya ce, maganar cewa duk wanda ya taɓa ku, ku zageshi, ku dake shi ba abin da za ayi, duk shirme ne wannan, ko kaɗan ba zai taimakawa al’ummar mu ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!