Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojan da ke samarwa ‘yan bindiga makamai ya shiga hannun hukuma

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa jami’an tsaro sun samu nasarar kama wani soja da budurwarsa wadanda ake zargin suna samarwa ‘yan bindiga makamai da alburusai da kakin soji.

Da ya ke zantawa da manema labarai a garin Gusau babban birnin jihar, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Zamfara, Dr. Bashir Muhammad Maru, ya ce, nan ba da jimawa ba, za a gano bakin zaren al’amuran tsaro a jihar, sakamakon asirin wasu da ke tonuwa.

Ya ce, sojoji ne suka samu nasarar kama daya daga cikinsu tare da budurwarsa wadanda suke zargin cewa karnukan farautar ‘yan bindiga ne.

Dr Bashir Muhammad Maru ya kuma ce an samu nasarar kama sojan ne sakamakon hadin kai da jama’a suka bai wa jami’an tsaro wajen basu bayanan sirri kan ayyukan batagari da ke cin kararsu ba babbaka a jihar.

‘‘Kamar yadda mai girma gwamna dama ya sha fada a baya na zargin cewa akwai batagari a kowanne bangare da ke taimakawa ‘yan bindiga, wannan kame da sojojin su ka yi, ya tabbatar da zargin da su ka yi tun da fari’’ a cewar Bashir Muhammad Maru.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!