Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojin Nijeriya sun ceto mutum 6 daga hannun ƴan bindiga

Published

on

Runduna ta daya ta sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wani dan bindiga 1 a jihar Kaduna.

Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Sojojin Runduna ta daya ta Sojojin Najeriya, Laftanar-Kanar Musa Yahaya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Asabar din nan, ya ce an ceto mutanen ne a ranar Juma’a.

Yahaya ya ce a ci gaba da aikin shara da dakarun rundunar ke yi na ci gaba da samun sakamako mai kyau.

Ya ce, “Rundunar ta yi aiki da sahihan bayanan da suka dace kan sace mutane 6 da aka yi a Hayin Tsando a yankin janaral Maraban Jos, a karamar hukumar Igabi ta jihar.

“Rundunar sojojin sun yi gaggawar tattarawa suka fara aikin bincike da ceto. Sojojin sun yi dauki ba dadi da ‘yan ta’addan da kuma masu aikata laifuka kuma an yi ta musayar wuta mai tsanani.

“A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar ceto mutanen shida da aka yi garkuwa da su, sun kama bindigu kirar AK 47 guda biyu tare da kashe dan bindiga guda daya yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga da dama.

“Babban Hafsan Sojan Najeriya shiyya ta daya kuma kwamandan rundunar Operation Whirl Punch, Manjo janaral Valentine Okoro, ya yabawa sojojin bisa jajircewar da suka yi.”

Yahaya ya kuma bukace su da su ci gaba da kai hare-hare har sai an kawar da duk wasu masu aikata laifuka a sashin ‘Yankin da ke ikonsu’ gaba daya.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya da su rika lura da wadanda suka samu raunukan harbin bindiga, sannan su kai rahoto ga rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro ‘yan uwa domin daukar mataki cikin gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!