Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar tarayyar Nijeriya ta fara karatu kan dokar cin tarar iyayen da basu saka ‘ya’yansu a makaranta ba

Published

on

Majalisar dattijan Nijeriya ta fara karanta wani kudirin doka da ke ba da shawarar cin tarar N50,000 ga iyayen da suka gaza wajen sanya ‘ya’yansu a makarantun firamare da sakandare.

Majalisar masu jar kujera ta ba da shawarar a bada abinci kyauta ga kowane yaro a ƙasar idan ya halaci makaranta.

Kudirin da wanda Sanata Orji Kalu ya gabatar mai taken, ‘Dokar ilimin bai daya na wajibi na shekarar 2004, sashi na 2’ ya bayyana cewa kowace gwamnati a Najeriya za ta samar da ilimi kyauta, na wajibi da na bai daya ga duk wani yaro da ya kai matakin firamare da karamar sakandare.

Dokar ta ci gaba da cewa duka iyaye su tabbatar da cewa yaransu sun halarta kuma sun kammala karatunsu na firamare da karamar sakandare ta hanyar kokarin tura yaron zuwa makarantun firamare da kananan sakandare.

Dokar ta ci gaba da cewa masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a karamar hukuma za su tabbatar da cewa duk iyaye ko mutumin da ke kulawa da yaro yzai yi aikin da aka dora masa a karkashin sashi na 2 (2) na wannan dokar.

Dokar ta kara da cewa, iyayen da suka saba wa umarnin da aka ba su zasu fuskanci tarar kudi kokuma dauri a gidan kaso.

Sai dai majalisar dattijai, a gyaran da ta yi, ta gabatar da shawarar tarar Naira 50,000, maimakon N5,000 da aka bayyana a baya a dokar.

Canjin ya ce, “Sashi na (4) (b) na babbar dokar an gyara shi ne ta hanyar cire N2,000 da saka sa N20,000. Sashi na (4) (c) na babban dokar an gyara shi ne ta hanyar cire N5,000 da saka N50,000.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!