Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji su sake bude sansanin sojojin ruwa na Baga don manoma su yi aikin su a yankin Tafkin Chadi – Zulum

Published

on

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bukaci Sojoji da su sake bude sansanin sojojin ruwa na Baga domin tabbatar da an bai wa manoma damar yin ayyukan su a yankin Tafkin Chadi.

Gwamna Zulum ya yi wannan kira ne yayin karbar sabon kwamandan rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai Manjo janar Christopher Musa a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

Wannan dai ya biyo bayan rokon da gwamna Zulum ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin ziyarar da ya kai jihar Borno a makon da ya gabata, inda kuma shugaban Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta samar tsaro ga noma musamman wadanda suka dawo daga gudun hijra don inganta rayuwar su.

Idan za a iya tunawa tun a watan Disambar 2018 ne mayakan Boko Haram suka kai hari sansanin sojojin ruwa da ke Baga tare da kwashe musu tarin makamai da alburusai daga ma’ajiyar makaman su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!