Labarai
Sojoji Sun Ceto Mutumin da Aka Sace a Kan Iyakar Kano da Katsina

Rundunar Sojin Ƙasar Nan ta yi nasarar ceto wani mutum da aka sace a kan iyakar Kano da Katsina da sanyin safiyar Lahadi, bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ‘yan bindiga daga wasu sassan jihar Katsina zuwa cikin Kano.
Ta cikin wata sanarwa da ya fitar, jami’in hulɗa da jama’a na Brigade ta 3 ta Rundunar Sojin Najeriya a Kano, Manjo Zubair Babatunde, ya bayyana cewa sojojin Joint Task Force Faruruwa sun yi artabu da ‘yan bindigar a yankin Ungwan Dogo da Ungwan Tudu, inda suka fatattake su zuwa cikin daji.
Jaridar Punch ta ruwato cewa a yayin fafatawar, an ceto Rabiu Alhaji Halilu mai shekara 38, wanda ya samu raunin harbi a kafa, kuma an kai shi cibiyar lafiya ta rundunar domin samun kulawa. Haka kuma, sojojin sun kwato babura uku da wasu shanu, yayin da aka ƙara tsaurara sintiri domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login