Labarai
Sojoji sun dakile wani mummunan hari a Najeriya

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun dakile wani yunkurin harin ‘yan ta’adda da aka kai kan gadar Azir Bridge da kuma garin Banki a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sani Uba, ya bayyana a wata sanarwa cewa maharan sun kai farmakin ne da safiyar Juma’a inda suka taso da yawa domin kwace sansanonin sojoji, amma sojojin sun tunkare su da karfi tare da mayar da martani cikin gaggawa.
Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun kaddamar da hare-hare na hadin gwiwa da suka tarwatsa tsarin harin ‘yan ta’addan tare da tilasta musu ja da baya. Haka kuma, rundunar sojin sama ta ba da gudunmawa ta hanyar kai hare-hare daga sama wanda ya taimaka wajen fatattakar maharan.
Rundunar ta kuma karyata rahotannin da wasu kafafen sada zumunta suka yada cewa ‘yan ta’addan sun kwace wuraren, tana mai cewa wannan farfaganda ce mara gaskiya. Ta tabbatar da cewa sojoji na ci gaba da rike iko a wuraren tare da kudurin kawar da barazanar ta’addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login