Labarai
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda tare da lalata cibiyar kera bama-bamai a Zamfara

Rundunar sojojin saman kasar nan NAF ta Operation Fansa Yamma, ta hallaka ’yan ta’adda da dama tare da lalata cibiyar kera bama-bamai da sansanonin su a jihar Zamfara.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sojojin saman, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a baya baya nan.
A cewar sa rundunar ta gudanar da hare-haren sama guda biyu masu tasiri a Dutsen Turba da kuma sansanin Kachalla Dogo Sule.
Dukkanin hare-haren an kai su ne a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, da aka kashe ’yan ta’adda da dama.
Air Commodore Ejodame ya ce bangaren sama na rundunar, bisa samun sahihan bayanan sirri daga tushe daban-daban, ta tura jiragen yakin NAF domin kai farmaki kan maboyar ’yan ta’adda a wuraren da aka gano.
You must be logged in to post a comment Login