Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Sojoji sun Kama mata 3 Yan kunar bakin wake a kauyen Kubtara

Published

on

A jiya  Lahadi ne Sojoji suka kama mata 3 ‘yan kunnar bakin wake, a yayin  da suke sintiri a kauyen Kubtara dake karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.

Hakan na dauke cikin sanarwar da darkatan yada labarai na rundunar Operation Lafiya Dole Kabal Onyema Nwachukwu ya fitar cewa, a yayin kamen sojojin sun gano makamai da kuma rigar da ake dauki da kayayyakin yin kunar bakin wake.

Onyema Nwachukwu ya kara da cewar,babban hafsan tsaron kasar nan Laftanan Janaral Tukur Buratai ya yabawa sojojin bisa wannan nasarar, yana mai karfafa musu gwiwa wajen cigaba da fatatakar kungiyar Boko Haram.

Wani cigaban kuma rundunar sojan kasar nan ta yi watsi da fefen fediyon da ake yada wa a kafafan sada zumunta na internet dake nuna wani sojan kasar nan na korafin rundunar na rashin makaman yaki ba gaskiya ba ne.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawon rundunar Sani Usman Kuka sheka ya fitar cewa fefen bediyon ya hasko sojan na cewa rundunar na fama da rashin makaman yaki da dai sauran su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!