Labarai
Sojoji sun kashe yan ta’adda 16 tare da kwato mutune 11 da aka sace

Dakarun Rundunar sojin Najeriya, sun hallaka yan ta’adda 16 tare da kwato mutune 11 da aka sace a yankin arewa maso gabashin kasar nan
Dakarun sun yi karam batta da ƴan ta’addan ne a yankin Gidan Kaji kan titin Maiduguri zuwa Damboa, inda suka kashe 16 daga cikinsu, abinda ya tilasta wa da dama tserewa da raunuka.
Sojin sun kuma ƙwato kekuna 20, da makamai da sauran kayayyaki da suke amfani dasu wajen kai hari.
Cikin sanarwar da jami’in yaɗa labaran rundunar haɗin gwiwar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a jiya Laraba, ya ce cikin ayyukan da suka gudanar har da daƙile harin mayaƙan ISWAP kan sansanin soji.
A cewarsa, sojin sun kuma kama wasu da ake zargin na safarar kayayyaki ga mayaƙan ISWAP, inda aka same su da ƙwayoyi da suka tsara kai wa ƴan ta’addan a yakin Bukarti.
You must be logged in to post a comment Login