Labarai
Sojoji sun kuɓutar da mata 12 da ƴan ta’addan ISWAP suka sace

Dakarun Operation Hadin Kai sun kubutar da ‘yan mata 12 da ƴan ta’addan ISWAP suka yi garkuwa da su a yankin Mussa, cikin ƙaramar hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno.
An sace yaran ne a ranar 23 ga Nuwamba, yayin da suke aikin girbi a gonakinsu. Harin da ‘yan ta’addan suka kai ya tilasta mazauna yankin da dama su tsere zuwa wasu kauyuka.
Shafin Zagazola Makama ya tabbatar da cewa aikin ceton ya gudana cikin nasara a ranar Asabar, duk da cewa har yanzu ba a san ko an biya fansa ba.
Dakarun sun ce shekarun yaran suna tsakanin 15 da 18, kuma an kaisu wurin soji domin bincike da duba lafiyarsu, kafin a sake haɗa su da iyalansu.
You must be logged in to post a comment Login